(ABNA24.com) Shugaban ya kuma shaidawa magoya bayansa cewa an duba masa huhunsa, kuma babu wata matsala a halin yanzu.
Dan shekaru 65, shugaba Bolsonaro, ana zarginsa da sakaci kan annobar ta korona, kuma na sha nuno shi a cikin jama’a baya sanye da takunkumin rufe baki da hanci, tare kuma da sukan matakan da wasu yankunan kasarsa ke dauka domin dakile yaduwar cutar.
Ko a jiya Litini, ya sake hawa kujerar na ki kan wasu kudurorin doka guda biyu na cilasta wa jama’a sanya takunkumi a wuraren dake fusknatar cinkoson jama’a.
Brazil, dai ita ce kasa ta biyu, bayan Amurka inda cutar ta fin illah a duniya, inda alkalumman baya bayan nan ke cewa mutum miliyan 1,6 cutar ta harba, yayin da kuma ta kashe mutum sama da dubu 65.
342/